Tonon Asiri Game Da Kaiwa Hadiza Gabon Kotu Akan Yaudarar Wani Matashi Sanadiyyar Soyayya Shahararriyar Jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta cewa ta san wani maβaikacin gwamnati mai suna Bala Musa mai shekaru 48 da haihuwa, wanda ya yi ikirarin cewa ta yi alkawarin aurensa bayan ya kashe mata N396,000. Jarumar wadda ta bayyana a gaban kotun shariβar musulunci a ranar Talata, a Magajin Gari Kaduna, ta shaida wa kotun cewa ba ta taba sanin mutumin da ake magana ba, kuma ba ta da wata alaka da shi. A makon da ya gabata ne mutumin ya shaida wa kotu cewa jarumar ta yi alkawarin aurensa, inda ya ce kawo yanzu ya kashe mata Naira 396,000. Amma da take magana ta bakin lauyanta Barista Mubarak Sani Jibril a harabar kotun, Gabon ta musanta zargin da ake mata. βBayan jin zarge-zargen nasa, a zahiri ta bayar da nata martanin wanda ba shakka a cewarta, ba ta taba haduwa da shi ba, ba ta taba sanin abin da ya faru ba. Ya hadu da ita a Facebook wanda ya ce mallakarta ne, don haka, ba mu ...
Comments
Post a Comment