An Buƙaci Na Zama ‘Yar Maɗigo (Lesbian) A Wani Film Din Kudanchi Cewar Rahama Sadau Shahararriyar jarumar fina-finan nan na Kannywood, Rahama Sadau, wacce aka kora daga masana’antar Kannywood a kwanakin baya, sananniya ce a gun yan kallo duba da irin tashen da tayi cikin kankanin lokaci daga zuwan ta masana’antar. Jarumar Ta gamu da tsautsayin da ya fada mataa masana’antar har ya jawo mata kora. tarihi dai ya nuna itace jarumar film ta farko da aka Taba korarta a masandantar. A wata hira da tayi da kafar yada labarai ta THE GUARDIAN, tauraruwa Rahama ta bayyana cewa an so tafito a wani fim din ta na kudu a matsayin yar madigo wato lesbian, amma sai ta ki yadda saboda la’akari da daga inda ta fito Wato arewachin Nigeria. da take tsokaci game da korar ta da kungiyar fina-finai tayi, Rahma Sadau tace ita wannan korar ma gaba ta kaita don kuwa yanzu idon ta ya kara budewa kuma ta kara samun wasu damanmaki na gudanar da sana’arta a dukkan fadin Duniya. Haka nan kuma ...
Comments
Post a Comment