DA DUMI DUMINSA: kuncin Rayuwa Zulum Ya raba kayan abinci Ga Magidanta Dubu 100,000 A Babban Birnin Maiduguri Anyi rabon ne da nufin rage wahalhalun da tashin farashin kayayyakin abinci. Zulum ya Gudanar da bikin baje kolin kayayyakin Masarufin A Yau Laraba a cibiyar wasanni ta Maiduguri. Kowanne daga cikin gidaje 100,000 ya samu buhu daya na shinkafa kilogiram 25 da buhun masara mai nauyin kilogiram 25. Da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da rabon kayayyakin, Zulum ya jaddada bukatar ci gaba da tallafa wa jama’a domin magance Wahalhalun da ake fuskanta Ya kuma jaddada aniyar Gwamnatinsa na ba da fifiko ga rayuwar jama’a, musamman wadanda ke fuskantar matsananciyar wahala Sakamakon rikicin Boko Haram. Zulum ya ci gaba da cewa: “Muna nan a yau ne domin kaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta dubu b100,000 daga Maiduguri Metropolitan da kewaye. Kowa a Najeriya ya san irin wahalhalun da mutane ke fuskanta dangane da karancin abinci da Hauhawar farashin kayyyaki Inji shi.
DA DUMI DUMINSA: kuncin Rayuwa Zulum Ya raba kayan abinci Ga Magidanta Dubu 100,000 A Babban Birnin Maiduguri
Anyi rabon ne da nufin rage wahalhalun da tashin farashin kayayyakin abinci.
Zulum ya Gudanar da bikin baje kolin kayayyakin Masarufin A Yau Laraba a cibiyar wasanni ta Maiduguri.
Kowanne daga cikin gidaje 100,000 ya samu buhu daya na shinkafa kilogiram 25 da buhun masara mai nauyin kilogiram 25.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kaddamar da rabon kayayyakin, Zulum ya jaddada bukatar ci gaba da tallafa wa jama’a domin magance Wahalhalun da ake fuskanta
Ya kuma jaddada aniyar Gwamnatinsa na ba da fifiko ga rayuwar jama’a, musamman wadanda ke fuskantar matsananciyar wahala Sakamakon rikicin Boko Haram.
Zulum ya ci gaba da cewa: “Muna nan a yau ne domin kaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta dubu b100,000 daga Maiduguri Metropolitan da kewaye. Kowa a Najeriya ya san irin wahalhalun da mutane ke fuskanta dangane da karancin abinci da Hauhawar farashin kayyyaki Inji shi.
Ga vedio 👇👇
Comments
Post a Comment