Wasu masu garkuwa da mutane don neman kuΙin fansa sun harbe Ιan uwansu yayin da suke yunΖurin garkuwa da wasu mutane a jihar. Lamarin ya faru ne a Ζauyen Yarimawa cikin karamar hukumar Tofa a jihar, inda gungun masu garkuwa da mutanen suka auka garin tsakar dare bisa babura Ιauke da munanan makamai. Wani mutum da lamarin ya faru a kan idonsa kuma ya buΖaci da ka da na ambaci sunansa, ya shaida wa BBc cewa miyagun sun dira a gidan wani mutum kuma nan take suka fasa kofar gidansa suka kama wasu. Sai dai suna ΖoΖarin tafiya da su ne mutum guda ya Ζwace ya gudu kuma a ΖoΖarin a harbe shi sai ‘yan bindigar suka kurkure suka dirka wa Ιan uwansu bindiga. An dai kama wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen ne, ta bin diddigin wayar mutumin da ya mutu, kasancewar ba su tafi da gawarsa ba. SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya ce suna bincike don gano sauran waΙanda ake zargi suna da hannu a wannan aika-aikar.''Mun kama wasu daga cikinsu, kuma sun aminc