An Kama Masu Gadin Makabarta Suna Tono Kaburburan Mutane
An Kama Masu Gadin Makabarta Suna Tono Kaburburan Mutane
Wasu masu gadin makabarta biyu sun shiga hannu inda aka kama su da kawunan dan Adam da suka hoto da cikin kabari.
Dubunsu ta cika ne bayan mutanen unguwa suka kama daya daga cikin mutanen [da ake kira Alhaji] da kawunan mutane a cikin jika.
Wani mazaunin unguwar ya ce, βJiya (Lahadi) da safe wani ya shiga jeji yin ba haya shiya sai ya ga Alhaji da wata katuwar guduma yana fasa wani kabari.
βDaga baya da Alhaji ya fito da wata jika sai mutumin ya daga kara, sai muka yi maza muka je; muka bincika sai muka ga kan mutun a cikin jikar.
Majiyar ta ce daga baya jamiβan tsaron Amotekun sun je sun binne kawunan a unguwar Surulere da ke garin Ondo, Jihar Ondo.
Kwamandan Rundunar [yankin Kudu maso Yamma] Amotekun, Cif Adetunji Adeleye ya tabbatar da tsare mutanen da ake zargin da ya ce jamiβansa sun iske mutanen unguwa na dab da aika su lahira.
Sai dai ya ce ba a samu kawunan mutane ba a tare da mutanen da aka kama kamar yadda ake zargi.
βJamiβanmu sun kubutar da mutanen da ake zargin ana dab da hallaka su, kuma mun mika su zuwa ga βyan sanda,β inji shi.
Danna vedion
ππππππ
Comments
Post a Comment