innalillahi Ku Kalli Halin Da Jaruma Hadiza Gabon Ta Shiga Akan Wannan Iftila'in Daya Faru Danna Hoton Kaga Cikakken Bayani


 

Tonon Asiri Game Da Kaiwa Hadiza Gabon Kotu Akan Yaudarar Wani Matashi Sanadiyyar Soyayya

Shahararriyar Jarumar Kannywood, Hadiza
Gabon, ta musanta cewa ta san wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa
mai shekaru 48 da haihuwa, wanda ya yi
ikirarin cewa ta yi alkawarin aurensa bayan ya kashe mata N396,000.



Jarumar wadda ta bayyana a gaban kotun
shari’ar musulunci a ranar Talata, a Magajin Gari Kaduna, ta shaida wa kotun cewa ba ta taba sanin mutumin da ake magana ba, kuma ba ta da wata alaka da shi.

A makon da ya gabata ne mutumin ya shaida wa kotu cewa jarumar ta yi alkawarin aurensa, inda ya ce kawo yanzu ya kashe mata Naira 396,000.

Amma da take magana ta bakin lauyanta
Barista Mubarak Sani Jibril a harabar kotun, Gabon ta musanta zargin da ake mata.



β€œBayan jin zarge-zargen nasa, a zahiri ta bayar da nata martanin wanda ba shakka a cewarta, ba ta taba haduwa da shi ba, ba ta taba sanin abin da ya faru ba.

Ya hadu da ita a Facebook wanda ya ce mallakarta ne, don haka, ba mu san komai ba game da hakan; mun saurare shi, za mu bar kotu ta yanke hukunci,” inji Mubarak.

Shima lauyan wanda ya shigar da karar,
Barista N. Murtala, ya ce wanda ake kyautata zaton masoyin wanda ya kasance vwanda yake karewa ne ya hadu da jaruma Gabon a Facebook, inda daga nan ne suka yi abota, inda ya kara da cewa ta yi alkawarin za ta aure shi kuma ya fara kashe mata kudi.



Ta musanta cewa ba ta san shi ba, amma mun sanar da kotu cewa za mu kawo shaidu kan hakan,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa ba su adawa da ba
da belin ta saboda laifin da ake iya bayar da beli ne.

Alkalin kotun, Khadi Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Yunin 2022 tare da bayar da belin ta da sharadin bayar da mutane biyu dake zaune a jihar.

Rahoton Fadeelah Omar Abdulmalik @Jarida Radio

A Wani Labarin Na Daban

Najeriya ta ce tana aiki da hukumomin da suka jiΙ“anci yaΖ™i da fasa-Ζ™waurin Ι—an’adam don ganin ta kwaso Ζ΄an matan Ζ™asar da aka kai su yin aikatau a gidajen masu hali na Ζ™asar IraΖ™i.

Ta ce tana fatan yin haka don ganin ta mayar da su gida Najeriya cikin aminci.

Hukumar yaΖ™i da fasa-Ζ™waurin Ι—an’adam ta Ζ™asar (NAPTIP) ta ce tana daΙ—a shiga damuwa saboda Ζ™aruwar β€˜yan matan Najeriya da ke shiga wahala a IraΖ™i.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Adekoye Vincent ya fitar ta ambato Babbar Daraktar Naptip tana bijiro da batun a lokacin da take jawabi game da sabbin wurare, da masu fasa-Ζ™waurin Ι—an’adam ke amfani da su a faΙ—in duniya wajen safarar β€˜yan Najeriya.

A baya dai, β€˜yan Najeriya suna zuwa ayyukan ci-rani da aikatau a Ζ™asashen Gabas ta Tsakiya da na yankin Gulf kamar Saudiyya da HaΙ—aΙ—Ι—iyar Daular Larabawa, amma ba a saba jin rahotannin kai β€˜yan Ζ™asar zuwa IraΖ™i ba.

Sai dai babbar daraktar Naptip, Fatima Waziri-Azi ta ce masu fasa-Ζ™waurin Ι—an’adam a yanzu sun karkata wajen kai β€˜yan Najeriya zuwa IraΖ™i don yin aikatau.

A cewarta, Ζ™oΖ™ari da ayyukan haΙ—in gwiwa wajen faΙ—akarwa da hukumarsu ke yi da wasu abokan Ζ™awance game da illolin fasa-Ζ™waurin Ι—an’adam zuwa wasu Ζ™asashe da aka sani, sun sanya masu fasa-Ζ™waurin karkata akala zuwa Ζ™asashe kamar IraΖ™i.



Fatima Waziri-Ari ta ce β€œMatan da aka yi safara zuwa IraΖ™i sun cika Naptip da roΖ™on a kuΙ“utar da su, kuma a mayar da su gida Najeriya, musamman daga biranen Baghdad da Basra.

Ta ce dillalan Ι—aukar aikin sun rarrraba β€˜yan matan gida-gida, inda su kuma suka je suka taras da rayuwar Ζ™asΖ™anci ta aikatau”.

Comments

Popular posts from this blog

An Kama Masu Gadin Makabarta Suna Tono Kaburburan Mutane

Innalillahi wa inna ilaihir Raji’un Masu garkuwa da mutane sun kashe Nabeeha saboda yan’uwan ta sun gaza hada kudin fansa Allah yajikan ta da rahama Dalibar ABU ZARIA 400Level Su Shida Aka Sace Tare Da Yan Uwanta Ita Sun Kashe Ta Yanzu Sauran Kannenta Guda Biyar Suna Hannu Su Don Allah Jama'a Ga Account Number A Taimaka A Kubutar Da Wadannan Kananan Yaran

DUNIYA BUDURWAR WAWA; Kalli jerin jaruman kannywood su 16 da kannywood ta juya musu baya suka zama abin tausayi.