Waiwaye Kan Lalacewar ‘Yam Mata A Kasar Hausa
Waiwaye Kan Lalacewar ‘Yam Mata A Kasar Hausa
Cikin Wani Dogon Bincike Da Kuma Kai Ziyara Wakilin Leadership Yayi A Gidan Gala Ya Samu Cikakken Rohoto Akan Tabarbarewar Tarbiyyar Yaran Hausawa A Gidan Gala (Gidan Dirama)
Matsalolin Da Ake Fuskanta A Gidan Gala
A ziyarar da wakilinmu ya kai zuwa gidan Dirama, idanunsa ya gane masa abubuwa daban-daban, sannan kunnensa ya jiye masa wasu daga ciki. Akwai abubuwan ban mamaki da ban tausayi gami da ban al’ajabi.
Abubuwan ban mamaki
Daga cikin abubuwan da ya gani na ban mamaki su ne, cin karo da cikakkiyar budurwa wacce da ka kalleta ba sai an yi maka bayani ba ka san gidansu akwai rufin asirin da ba rashi ne ko talauci ya kawo ta gidan ba, sannan kuma kuma za ka ga budurwar da idanka dube ta ka san ba rashin masoyi ne ya kawo ta wannan wuri ba, saboda irin kyan halittar da Allah ya yi mata.
Wata kuma za ka ganta ita ba kyau ba, babu cikakkiyar sutura sannan kuma ga kwarewa a tantiranci, domin a ganinta idan ba ta yi irin wannan zakewar ba kamar ba za ta samu kasuwa ba.
Abin Tausayi
Wani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru, da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.
Za ka ga mutum wanda a haife ya yi jika da ita, amma ba shi da burin da ya wuce ya ga kusance da kwanciya.
تعليقات
إرسال تعليق