Murja ba ta halarci makarantar boko ba amma ta yi makarantar Islamiyya ta Fodiyya da ke cikin garin Kunya, ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano. Tun bayan kamun da hukumar Hizba ta Kano ta yi wa fitacciyar ƴar Tiktok din nan a arewacin Najeriya, Murja Kunya, da kuma gurfanar da ita gaban kotu a inda aka aike da ita gidan gyaran hali, al'amura suke ta faruwa dangane da ita. Babban batun da ya fi ɗaukar hankalin al'ummar Kano da arewacin Najeriya shi ne yadda aka saki Murjar ta bar gidan gyaran hali, wani abu da ya sa aka yi ta zargin jami'an gwamnatin Kano. To sai dai gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce sam ba ta da masaniyar yadda Murja ta fice daga gidan gyaran halin, inda mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce "kujerar gwamna ta fi karfin mayar da hankali kan wannan batu". Da safiyar Talata ne kuma wata kotu a Kano ta aike da Murjar zuwa asibitin masu larurar kwakwalwa har na tsawon watanni uku domin a "duba lafiyar kwakwalwarta"