Rahotanni daga ƙasar Saudi Arabia na cewa jami'an tsaron ƙasar sun cafke mutumin da ya zagi Nana Aisha matar MANZON ALLAH SAW a harabar masallacin Madina a lokacin da suke muhawara da wani ɗan ƙasar Pakistan Jaridar Labaran Hausa ta ruwaito cewa. Rundunar ‘yan sanda a birnin Riyadh ta tabbatar da kama wani mutumi wanda ya zagi Sayyada Aisha R.A, matar Annabi Muhammad (SAW). Manjo Khaled Al-kraidis, wanda yanke shine kakakin rundunar ‘yan sandan Riyadh, ya bayyana cewa a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sadarwa, an gano cewa bidiyon cin mutuncin ne ga Annabi Muhammad (SAW), haka kuma zagi ne ga uwar muminai, Aisha (R.A). Bayan kama mutumin an gabatar dashi a gaban kotu domin yanke masa hukumcin daya dace da shi. An wallafa bidiyon ne a shafukan sadarwa a ranar 10 ga watan Muharram, a lokacin da ‘yan kungiyar Shia suke nuna bakin cikinsu kan kisan da aka yiwa Sayyadina Hussain a lokacin yakin Karbala. A Musulunci, duka matan Annabi Muhammad guda 11 ana daukar su a matsayin iya