Davido ya goge bidiyon rawa a masallaci bayan ya sha caccaka Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya Sanannen mawaki a Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge bidiyon waka mai cike da ce-ce-ku-ce na wani yaronsa, Logos Olori, bayan ya fuskanci suka a intanet. A ranar Asabar, Davido ya fuskanci suka daga Musulmai da yawa a shafukan sada zumunta saboda ya yada tallar dakika 45 ta bidiyon wakar a shafinsa na Twitter. Bidiyon wanda musulmai da dama suka bayyana a matsayin abin takaici, ya nuna wasu gungun maza sanye da sutura irin ta musulmai, suna sallah da addu'o'i, amma ba zato ba tsammani sai suka ɓarke da rawa da waka. Sun zargi mawakin da rashin mutunta addinin Islama ta hanyar hada ayyukan addini da waka da raye-raye. Sun kuma yi kira gare shi da ya goge bidiyon tare da bayar da hakuri. Fitattun ‘yan Najeriya irin su Bashir Ahmad da Ali Nuhu sun tofa albarkacin bakinsu kan hakan. Yayin da mawaki