Mawaƙin Najeriya Davido ya goge waƙar mai suna ‘Jaye Lo’, wadda aka nuna masu sallah sun ɓarke da rawa, bayan ya wallafa ta a ranar Asabar. Karanta ƙarin bayani a nan:




 Davido ya goge bidiyon rawa a masallaci bayan ya sha caccaka




Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Sanannen mawaki a Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya goge bidiyon waka mai cike da ce-ce-ku-ce na wani yaronsa, Logos Olori, bayan ya fuskanci suka a intanet.

A ranar Asabar, Davido ya fuskanci suka daga Musulmai da yawa a shafukan sada zumunta saboda ya yada tallar dakika 45 ta bidiyon wakar a shafinsa na Twitter.

Bidiyon wanda musulmai da dama suka bayyana a matsayin abin takaici, ya nuna wasu gungun maza sanye da sutura irin ta musulmai, suna sallah da addu'o'i, amma ba zato ba tsammani sai suka ɓarke da rawa da waka.

Sun zargi mawakin da rashin mutunta addinin Islama ta hanyar hada ayyukan addini da waka da raye-raye.

Sun kuma yi kira gare shi da ya goge bidiyon tare da bayar da hakuri.




Fitattun ‘yan Najeriya irin su Bashir Ahmad da Ali Nuhu sun tofa albarkacin bakinsu kan hakan.

Yayin da mawakin ya yi shiru kan lamarin kuma bai bayar da hakuri a hukumance ba, kwanaki biyu bayan ƙorafe-ƙorafen, a karshe Davido bayan ya sha matsin lamba ya goge bidiyon.

Ga vedion

👇👇👇👇👇



تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

DUNIYA BUDURWAR WAWA; Kalli jerin jaruman kannywood su 16 da kannywood ta juya musu baya suka zama abin tausayi.

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Yanzu Yanzu Anga Jijirin Wata Ramadan a Kasar Saudiyya Gobe Insha Allahu Zamu Tashi Da Azumi Wata Ramadan Kareem Ya Allah Duk Alkhairin Dake Cikin wannan Wata Allah Ubangiji Kasadamu Dashi Sharrin Kuma Dake Cikinsa Allah Ubangiji Ya Karemu Ya Allah Kasa Muda Daga Cikin Bayinka Wadanda Kake Yan Tawa A Cikin Wannan Wata Mai Albarka Alfarmar Annabi Muhammad S 💔 A 💔 W 💔 Ameeeen Thumma Ameeeen 🤲🤲🤲