An cinna wa ofishin INEC na Takai wuta a Kano Ƙarin bayani
INEC ta ƙaddamar da ɗakin tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa
Wannan shafi zai rinƙa kawo maku bayanai kan abubuwan da suke faruwa a faɗin Najeriya game da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya.
Related Video and Audio
VIDEO 1 MINUTE 9 SECONDSVIDEO 1 MINUTE 9 SECONDS1:09
Play video Runfunan zaɓe a Najeriya: Wani wurin fayau, wani kuma a cunkushe from BBCRunfunan zaɓe a Najeriya: Wani wurin fayau, wani kuma a cunkushe
BBC
Play video Runfunan zaɓe a Najeriya: Wani wurin fayau, wani kuma a cunkushe
Play video Rahoto from BBCRahoto
BBC
Play video Rahoto from BBC
Takaitacce
INEC ta ƙaddamar da zauren tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa
Ma'aikatan INEC na tururuwar kai sakamakon zaɓe a Kano
Ana samun jinkiri wurin tattara sakamakon zaɓe a wasu yankuna a Kano
Gwamnan Borno ya yi alƙawarin bai wa 'yan kasuwar da gobara ta shafa tallafin N1bn
Jami'an zaɓe na jiran INEC ta fara karɓar sakamako a Adamawa
Yadda aka ci gaba da aikin zaɓe da daddare a Najeriya
Ana tattara sakamakon zaɓe a Najeriya
Zaɓen Najeriya 2023: Rahotannin tarwatsa rumfunan zaɓe a wurare daban-daban
Rahoto kai-tsaye
Daga Haruna Kakangi, Buhari Muhammad Fagge, Abdullahi Bello Diginza, Yusuf Yakasai da Nabeela Mukhtar Uba
An wallafa a 14:0714:07
SHAREDAn cinna wa ofishin INEC na Takai wuta a KanO
Wani ginin INEC da wuta ta ci a jihar Plateau, wanda shi ma a baya aka ƙonaImage caption: Wani ginin INEC da wuta ta ci a jihar Plateau, wanda shi ma a baya aka ƙona
Hukumar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa an cinna wa ofishin hukumar zaɓe ta ƙasar reshen ƙaramar hukumar Takai wuta.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.
'Ƴan banga ne suka cinna wa janareton da ake aiki da shi a cibyar wuta, lokacin da suka shiga wajen ta baya, amma ba wani ci ta yi ba, kuma an kashe ta, tuni muka ƙara yawan jami'anmu a wajen,' in ji Kiyawa.
BBC ta tuntuɓi wani ganau wanda ya ce an cinna wutar kuma ta ƙona wasu robobi da aka zuba takardun ƙuri'un da aka ƙada amma ba ta ƙona wajen da ake aikin ƙirga ƙuri'u ba.
تعليقات
إرسال تعليق