Masu garkuwa da mutane sun harbe ɗan uwansu a Kano
Wasu masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa sun harbe ɗan uwansu yayin da suke yunƙurin garkuwa da wasu mutane a jihar.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Yarimawa cikin karamar hukumar Tofa a jihar, inda gungun masu garkuwa da mutanen suka auka garin tsakar dare bisa babura ɗauke da munanan makamai.
Wani mutum da lamarin ya faru a kan idonsa kuma ya buƙaci da ka da na ambaci sunansa, ya shaida wa BBc cewa miyagun sun dira a gidan wani mutum kuma nan take suka fasa kofar gidansa suka kama wasu.
Sai dai suna ƙoƙarin tafiya da su ne mutum guda ya ƙwace ya gudu kuma a ƙoƙarin a harbe shi sai ‘yan bindigar suka kurkure suka dirka wa ɗan uwansu bindiga.
An dai kama wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen ne, ta bin diddigin wayar mutumin da ya mutu, kasancewar ba su tafi da gawarsa ba.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ya ce suna bincike don gano sauran waɗanda ake zargi suna da hannu a wannan aika-aikar.''Mun kama wasu daga cikinsu, kuma sun amince cewa su ne suka aikata wannan laifi, sannan suka harbe ɗan uwansu'', in ji shi.
Ya ce mutanen na hannun 'yan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.
Bayanai na cewa mutum guda da masu garkuwar suka ta fi da shi dai, daga bi-sani ya kuɓuta.
Jihar Kano ta yi ƙaurin suna a ayyukan ‘yan daba da ‘yan bangar siyasa amma garkuwa da mutane wani sabon al’amari ne da ke neman zama ruwan dare a yankunan jihar musamman a baya-bayan nan.
Abin da yasa jami’an tsaro suka ce sun tashi haiƙan don daƙile matsalar.
Inda kuma suka nemi haɗin kan jama’a wajen bayar da bayanan da za su taimaka wajen kama masu aikata wannan laifi.
تعليقات
إرسال تعليق