Jama'ar gari sun wawushe kayan abinci daga wata tirelar kamfanin Dangote a Jihar Katsina.

 


Jama’ar gari a Jihar Katsina sun daka wa wata motar kamfanin Dangote wawa, inda suka yi awon gaba da kayan abincin da take dauke da su.

Hakan ta faru ne a yayin da matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi a Najeriya suka kai makura, inda kudin buhun masara ya kusa ninka mafi karancin albashi.

A bidiyon wasoson da ke yawo a kafofin sada zumunta, an ga maza da mata da kananan yara suna daukar buhunan kayan abinci suna awon gaba da su daga babbar motar da ke kan babbar hanya.

Wasu daga cikin mutanen kuma suna kokawar daukar buhunan abincin, da ake zargin za a kai kasar Jamhuriyar Nijar ne.

Amma a sanarwar kamfanin da ke tabbatar da aukuwar lamarin, kamfanin na Dangote ya musanta cewa Nijar zai kai kayan abincin.

A shekarar da ta gabata ne Najeriya ta rufe iyakarta da Nijar sakamakon hambarar da Shugaba  Mohamed Bazoum da sojojin kasar suka yi.




تعليقات

المشاركات الشائعة من هذه المدونة

DUNIYA BUDURWAR WAWA; Kalli jerin jaruman kannywood su 16 da kannywood ta juya musu baya suka zama abin tausayi.

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Yanzu Yanzu Anga Jijirin Wata Ramadan a Kasar Saudiyya Gobe Insha Allahu Zamu Tashi Da Azumi Wata Ramadan Kareem Ya Allah Duk Alkhairin Dake Cikin wannan Wata Allah Ubangiji Kasadamu Dashi Sharrin Kuma Dake Cikinsa Allah Ubangiji Ya Karemu Ya Allah Kasa Muda Daga Cikin Bayinka Wadanda Kake Yan Tawa A Cikin Wannan Wata Mai Albarka Alfarmar Annabi Muhammad S 💔 A 💔 W 💔 Ameeeen Thumma Ameeeen 🤲🤲🤲